1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19 da muhalli sun mamaye taron G7

Abdoulaye Mamane Amadou
June 11, 2021

Kasashe masu karfin tattalin arziki G7 na gudanar da taron kolinsu a Birtaniya da zimmar tattauna batutuwan corona da muhalli da ma tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3ujvm
Großbritannien G7 l US Präsident Biden trifft PM Johnson in Cornwall
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Taron da zai shafe tsawon kwanaki uku daga wannan Jumma'a, zai fi mayar da hankali ne kan batutuwan raba daidai na alluran rigakafin corona da sauyin yanayi da kuma batun farfado da tattalin arzikin kasashen.

Sai dai ana hasashen cewa firaministan Indiya Narendra Modi, zai halarci taron ne ta kafar bidiyo kai tsaye, sabanin takwarorinsa na Amirka da Birtaniya da Canada da Jamus da Italiya da Faransa da Japan, da za su yi ganawar ta bayyane a yau din nan.

Fiye da 'yan sanda 6500 ne dai aka tanada a cikin shirin ko takwana don kwantar da tarzomar masu zanga-zanga