1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20: Bunkasa dabarun samar da makamashi

September 9, 2023

Shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya G20 sun cimma matsayar bunkasa sabbin dabarun makamashi mara gurbata muhalli.

https://p.dw.com/p/4W9Iy
Taron kungiyar G20 da ya gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya
Hoto: Russian Foreign Ministry Press Service/TASS/dpa/picture alliance

Kungiyar G20 ta kuma ce za ta kara yawan tallafin da suke bayar wa ga wadanda suka fi fuskantar tasirin sauyin yanayi.

Karin bayani:  An bude taron kungiyar G20 na bana

A taron na da shugabannin kasashen da ke fitar da kaso mafi yawa na hayaki mai gurbata muhalli a duniya suka kammala a birnin Delhi na kasar India, guda daga cikin manyan jami'an gwamnatin Indiya da ke zama mai masaukin baki na taron na bana, Amitabh Kant ya ce, matsayar ita ce mafi mahimmanci a daftarin matakai kan tasirin sauyin yanayi.

Duk da yawancin kwararru kan yanayi ba su nuna farin cikinsu ba, sai dai ana ganin shugabannin G20din sun bada babban sako kan daukar matakai yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar bala'oi da suka shafi sauyin yanayi.