1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fusata bayan zanga-zangar garin Chemnitz

Suleiman Babayo MAB
August 30, 2018

Mahukunta na kasar Jamus ma neman hanyar shawo kan zanga-zanga da fusata da mutane suka nuna bayan kisan da wasu 'yan gudun hijira suka yi wa wani matashi dan shekaru 35 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/342YQ
Chemnitz - Proteste der Rechten mit Plakat mit blutigen Frauengesichtern
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Meyer

A wannan Alhamis gwamnan jihar Lower Saxony Michael Kretschmer ya kai ziyara zuwa garin na Chemnitz, inda mutane suka nuna matukar fusata bayan kisan da wasu 'yan gudun hijira biyu suka yi wa wani matashi dan shekaru 35 da haihuwa, kuma ake ci gaba da gudanar da bincike a kai. Shi dai gwamnan  Michael Kretschmer ya kasance daya daga cikin masu danganta ta kut da kut da shugabar gwamnati Angela Merkel.

Kusan mutane 20 suka jikkata lokacin da zanga-zangar da masu matsanancin ra'ayin da ke nuna kyama ga baki suka shirya. Lamarin da shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al-Hussein ya nuna kaduwa a kai:

Seid Al-Hussein
MDD ta nuna damuwa kan zanga-zangar kyamar baki a ChemnitzHoto: Reuters/P. Albouy

 Ya ce: " Ina nufin irin hotuna da ake gani masu tayar da hankali ne. Ana sake ganin mutane suna gaisuwa irin na 'yan Nazi a kasashen da ya dace ake da masaniya kamar Jamus, da ya kamata ana da wayewa kan wahalhalun da aka shiga a kasashen Turai a baya. Amma ganin mutane a Jihar Lower Saxony a 'yan kwanakin da suka gabata abun na da kaduwa."

Tuni hukumomi suka karyata wani sabon bidiyo da yake yawo a kafofin Intanet cewa an kashe mutumin dan shekaru 35 lokacin da yake kare wata mata daga cin zarafi. Masu zanga-zangar nuna kiyayya ga bakin sun yi bakaken kalamai tare da cewa suna da yawa kuma suna da karfi.

A cewar shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al-Hussein abubuwan da suke faruwa ba sa nuna wata mokama mai kyau, inda ya ce "Wasu lukuta lamarin yana sanyaya gwiwa saboda karuwar kungiyoyin siyasa masu matsanancin ra'ayi wadanda kuma ba su da wata manufa ta dogon lokaci, wannan shi ne abin da muke fada."

Deutschland Tatort in Chemnitz
Jama'a na nuna alhini dangane da kashe matashi a ChemnitzHoto: picture-alliance/dpa/J.Woitas

  Jami'in ya bukaci samun karin 'yan siyasa wadanda za su yi yaki da matsanancin ra'ayi. Sai dai kimanin mutane 150 masu ra'ayin gaba-dai gaba-dai sun gudanar da jerin gwano a garin Dresden na rashin yarda da duk wani ra'ayin na nuna kyama.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa an cafke matasa biyu bisa zargin aikata kisan, daya dan shekaru 22 daga kasar Iraki kana daya daga Siriya dan shekaru 23 da haihuwa. Wannan lamari ya fara haifar da nuna kiyayya inda hukumomi suka ce a wannan Alhamis wasu sun kai farmaki kan wani dan Siriya dan shekaru 20 da haihuwa a garin Wismar inda mutane suka yi bakaken kalamai kan baki, kuma yanzu haka yana asibiti saboda raunukan da ya samu.