1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW: Fursunoni na wahala a Iraki

Abdul-raheem Hassan
July 4, 2019

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce fursunoni na cikin mawuyacin hali sakamakon cinkoso da rashin walwala da suke fuskanta a gidajen yarin kasar Iraki.

https://p.dw.com/p/3LavM
Irak - Gefängnis Abu Ghraib
Hoto: Getty Images

A cewar kungiyar Human Rights Watch dubban mutane da ke tsare a yawancin kurkuku na cikin hatsarin kamuwa da cututtuka sakamakon rashin tsabta.

Kungiyar ta ce akwai hotunan da ke nuna munin yanayin rayuwa da fursunonin ke ciki a gidajen yarin kasar, ciki har da gidajen gyara halinka na kananan yara da mata ke tsare.

Gwamnatin Bagadaza ta yi ikirarin karya lagon mayakan IS a shekarar 2017 kuma yawancin fursunonin da ke kulle a gidajen kason kasar mayakan IS ne da ake zargi da ayyukan ta'addanci.