1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frime Ministan Togo ya yi murabus

July 13, 2012

Frime Ministan Togo ya yi murabus tare da majalisar ministocinsa, kawo yanzu dai babu ƙwaƙwarar dalili, illa sanarwar da ta ce shugaban ƙasa ya amince da matakin

https://p.dw.com/p/15Wyy
Gilbert Fossoun Houngbo, Prime Minister of Togo, addresses the 65th session of the United Nations General Assembly at U.N. headquarters Friday, Sept. 24, 2010. (ddp images/AP Photo/Jason DeCrow)
Gilbert Fossoun Houngbo - Frime Minista mai murabusHoto: AP

A wani mataki na ba zata, wanda ya baiwa al'ummar ƙasar Togo mamaki, Frime Ministan ƙasar da gwamnatinsa sun yi murabus ranar alhamis. Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban ƙasa, wadda bata bada wasu dalilai masu ƙwari dangane da saukar Frime Minista Gilbert Fossoun Houngbo da majalisar ministocinsa ba, ta bayyana cewa shugaban ƙasa Faure Gnassingbe, ya anshi takardar murabus din ta su kuma ya amince da ita.

Wannan murabus na zuwa ne bayan da zanga-zangar nuna ƙyamar gwamnati ya ƙaru a tsakanin 'yan kwanakin baya-bayan nan, wato gabanin zaɓukan ƙananan hukumomi da na 'yan majalisar dokokin da ake sa ran gudanarwa a watan Oktoba idan Allah ya kai mu.

Iyali guda ne dai ke jagorancin ƙasar ta Togo da ke yankin yammacin Afirka na kusan shekaru 50 yanzu.

Shugaban ƙasar da ke mulki yanzu ya karɓi iko ne a shekarar 2005 bayan rasuwar mahaifinsa daɗaɗɗen shugaban mulkin kama karyar ƙasar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas