1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frime Ministan Rasha na ziyara a China domin inganta dangantakar ƙasashen biyu

October 11, 2011

Ƙasashen Rasha da China sun yi alƙawarin faɗaɗa dangantakarsu ta fannin tattalin arziki ta hanyar kafa gidauniyar da za ta tallafa masu.

https://p.dw.com/p/12qFP
Frime Ministan Rasha Vladimir Putin, da shugaba Wen Jiabao na ChinaHoto: AP

Ƙasashen China da Rasha suna neman inganta dangantakarsu a fannin tattalin arziki. A wata ziyarar da ya kai Beijing babban birnin Chinan, Frime Ministan Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga ɓangarorin biyu da su hada hannu domin kafa wata gidauniya inda za su zuba jari na miliyoyin dala. Fiye da kashi biyu cikin uku na kuɗin zai je wajen tallafawa Rasha da ƙasashen da ke maƙotaka da ita kamar su Kazakstan da Belarus. A yayin da sauran za su je ga China a cewar tawagar ta Rasha. Da farko dai shugaban gwamnatin China Wen Jiabao ya tattauna da Putin a babban zauren alumma. Putin ya tabbatar da cewa an shiga zagayen ƙarshe na tattaunawar da Rashan ke yi da jamhoriyar al'ummar Chinan dangane da aika mata iskar gas, tun kimanin shekaru biyar da suka wuce. Haka nan kuma ana sa ran rattaba hannu a kan kwangilar da za ta tabbatar da hakan a wannan Talatar.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Usman Shehu Usman