1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamnista Victor Ponta na Romaniya ya yi murabus

Suleiman BabayoNovember 4, 2015

Gwamnatin Ponta tana karkashin matsin lamba bisa zargin cin hanci da gobara a gidan rawa da ta hallaka mutane 32 yayin da wasu kusan 200 suka samu raunika a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/1GzTT
Rumänien Victor Ponta in Bukarest
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Ghement

Firaminista Victor Ponta na Romaniya ya bayyana ajiye aiki yayin da gwamnati ke fuskantar tuhuma kan cin hanci da rashawa, da mutuwar mutane 32 sannan wasu kusan 200 suka samu raunika a gobarar da ta tashi a wani gidan rawa da ke birnin Bucharest fadar gwamnatin kasar. Wannan ajiye aiki ya zo kwana daya bayan fiye da mutane dubu 20 sun yi zanga-zangar neman Ponta ya yi murabus. Masu zanga-zangar sun danganta gobarar da aka samu da cin hanci da ke dakile abubuwa da gwamnati ya dace ta aiwatar.

Tun shekara ta 2012 Firaminista Ponta dan shekaru 43, yake rike da madafun iko, kuma daga watan Satumba lamura suka fara dagulewa sakamakon zargin gwamnati da karya dokokin haraji da halarta kudaden haramun.

Shugaba Klaus Iohannis na kasar ta Romaniya zai sake mika sunan sabon firaminista domin majalisar dokoki ta amince sannan a kafa gwamnati.