1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Firaminista Sheikh Hasina ta arce Indiya

Abdullahi Tanko Bala AH
August 5, 2024

Firaministar kasar Bangladesh Sheikh Hasina ta yi murabus abin da ya kawo karshen shekaru 15 da ta kwashe tana mulki, a daidai lokacin da dubban 'yan zanga-zanga suka bijire wa dokar hana fita.

https://p.dw.com/p/4j81w
Hoto: Manish Swarup/AP/picture alliance

 Abin da ya faro a matsayin zanga-zangar lumana ta dalibai a Bangladesh game da kaso kan rabon ayyukan gwamnati a watan Yuli a karshe ta rikide zuwa tarzomar da ta yi awon gaba da gwamnatin ta Sheikh Hasina inda ta yi murabus ta fice a jirgin helikopta na soji. Babban hafsan sojin Bangladesh din Janar Waker-Uz-Zaman ya ce zai nemi sahalewar shugaban kasa domin kafa gwamnatin rikon kwarya. A Jawabin da ya yiwa al'umar kasar ya bukaci jama'a su kwantar da hankula.

Bangladesch | Proteste und Ausschreitungen
Hoto: MD Mehedi Hasan/ZUMA/picture alliance

" Firaminista ta yi murabus. A yanzu za mu kafa gwamnatin rikon kwarya don ci gaba da jagorantar kasarmu." A Dangane da bukatar masu zanga-zangar ta yin adalci ga kashe-kashen da suka faru. Babban hafsan sojin Janar Waker Uz Zaman ya yi bayani da cewa. '' Ina tabbatar muku da cewa za mu yi adalci ga wannan hasarar rayuka da ya faru. Ku ba da amanna ga sojoji, na dauki alkawarin kare rayuka da dukiyoyinku. Ina tabbatar muku da cewa ba  zan baku kunya ba."

Bangladesch | Proteste und Ausschreitungen
Hoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS

Shin me ya jawo daliban yin zanga-zanga? Da farko dai zanga- zangar kan rabon wani kaso ne da gwamnati ke warewa na guraben ayyukan gwamnati inda aka kebe  kashi 30 cikin dari ga iyalan mutanen da suka yi gwagwarmayar kwatar yancin Bangladesh daga kasar Pakistan a 1971. Masu zanga-zangar suka ce wannan wani na'ui ne na wariya ko nuna bambanci kuma tsarin ya fi amfanar magoya bayan jam'yyar Awami League ta firaminista Sheikh Hasina, jam'iyyar da ta jagoranci samun yancin a  wancan lokaci.

Bangladesch | Proteste und Ausschreitungen
Hoto: Munir Uz Zaman/AFP/Getty Images

Wannan dambarwa dai ta nuna tsantsan halin da kasar ta Bangaldesh ta fada ciki na matsin tattalin arziki, da karancin kudaden ajiya na kasar waje da rasahin aikin yi ga matasa wadanda ke neman aiki mai gwabi na gwamanti. Sai dai da tarzomar ta ci gaba a watan da ya gabata, sai kotun kolin kasar ta rage kason aikin da ake warewa iyalan 'yan mazan jiya daga kashi 30 zuwa kashi 5 cikin dari, ta ce a mika kashi 93 cikin dari na guraben ayyukan ga wadanda suka cancanta, ragowar kashi biyu cikin dari kuma ga tsirarun kabilu da masu bukata ta  musamman.

Bangladesch | Proteste und Ausschreitungen
Hoto: Joy Saha/ZUMA/IMAGO/ZUMA

Gwamnatin ta amince da niyyar cewa lamarin zai lafa to amma sai zanga-zangar ta ci gaba da habaka tare da wasu sabbin bukatu cewa dole a gudanar da bincike kan dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi da haddasa mutuwar mutane da dama sannan a karshe ma da bukatar gwamnatin ta Hasina da sauka daga karagar mulki. Gwamnatin dai ta sha yin kokarin murkushe zanga-zangar da ta dora alhakin zangon kasa daga Jam'iyyun adawa. Sai dai lamarin ya yi kamari inda maimakon kwantar da tarzoma, jami'an tsaro suka harba alburusai da kafofin yada labarai na cikin gida suka ce mutane kusan 300 suka rasa rayukansu a zanga-zanga a fadin kasar, gwamnatin dai ta dauki dokar takaita zirga-zirgar jama'a da katse kafofin sadarwar Internet, to amma wadannan tsauraran matakai maimakon tarnaki sai su kara tunzura zanga-zangar.Dubban masu zanga-zanga cikin shewa da murna sun afka fadar firaministar ta Bangladesh Sheikh Hasina bayan da ta fice daga kasar yayin da zanga-zangar adawa da gwamnatin ta kai kololuwa, wasu na kwasar ganima. Dandazon mutanen dauke da tutoci suna raye-raye a titunan Dhaka. A yanzu dai yayin da aka janye 'yan sanda daga tituna an kuma dawo da Internet. Dubban jama'a sun bazama tituna suna murna da sambarka da murabus din firaministar. Wani na hannun daman tsohuwar firaministar ta Bangladesh, ya ce Sheikh Hasina mai shekaru 76 da haihuwa ta sauka birnin Agartala da ke arewa maso gabashin  Indiya.

Bangladesch Menschen feiern den Rücktritt von Premierministerin Hasina in Dhaka
Hoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS
 Sheikh Hasina
Sheikh HasinaHoto: PID Bangladesh