1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fumio Kishida ya tsallake rijiya da baya

Abdullahi Tanko Bala
April 15, 2023

An gaggauta ficewa da firaministan Japan Fumio Kishida daga wani zauren taro bayan wani hari da aka kai masa da konson bam na hayaki a birnin wakayama a lokacin wani yakin neman zabe

https://p.dw.com/p/4Q7rl
Japan | Zwischenfall beim Besuch von Fumio Kishida in Wakayama
Hoto: Kyodo/REUTERS

An jefi Firaministan Japan Fumio Kishida konson bam na hayaki yayin da yake dab da gabatar da jawabi a wajen wani taron yakin neman zabe a a garin Wakayama da ke gabashin Japan a wannan Asabar.

Firaministan dai bai sami rauni ba kuma 'yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi bayan aukuwar lamarin.

A watan Yulin bara ma haka aka harbi tsohon firaministan kasar Shinzo Abe inda ya sami mummunan rauni a lokacin da yake gabatar da jawabi a birnin Nara.