1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Isra'ila ya yi kiran taron dangi kan Iran

Yusuf Bala Nayaya
February 5, 2017

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana sanya sabbin takunkumi kan kasar ta Iran bayan gwajin makami mai linzami.

https://p.dw.com/p/2X0Ze
Israel Premierminister Benjamin Netanjahu
Hoto: Reuters/B. Ratner

Firaministan kasar Isra'ila  Benjamin Netanyahu ya yi kira na neman hadin kan kasa da kasa dan taron dangi kan kasar Iran, abin da ke zuwa bayan da mahukuntan na birnin Tehran suka yi gwaji na makami mai linzami.

Netanyahu ya yi wannan kira ne a ranar Lahadin nan gabanin kama hanya zuwa birnin London na Birtaniya inda zai gana da takwararsa ta Birtaniya Theresa May  a kokarinsu na fadada dangantarsu ta diplomasiya da tsaro da tattalin arziki da fasaha.

"A yanayi na diplomisiya , ina so na kara kira na samun hadin kai a yi baki daya kan kasar ta Iran wacce a 'yan kwanakin nan ke daga hancinta, wannan abu ne da ya zama dole a yi shi musamman ganin yadda kasar ta Iran ke keta umarni na kasa da kasa."

Kasar Iran dai da Isra'ila ba a ga miciji tsakanin juna, a shekarar 2015 baro-baro  Netanyahu ya fito tare da nuna adawarsa da shirin janye wa Iran takunkumi na kasashen Yammacin Duniya inda ya ce kasar ba za ta tsaya ba a shirinta na kokarin mallakar makamin nukiliya.