1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Firaministan Birtaniya yana ziyara a Jamus

Suleiman Babayo USU
April 24, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai karbi bakuncin Firaminista Rishi Sunak na Birtaniya wanda yake zuwa birnin Berlin a kafon farko tun lokacin da ya dauki madafun iko watanni 18 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4f7kJ
Taron kungiyar G7 a Hiroshima  da ke Japan | Rishi Sunak da Olaf Scholz
Firaminista Rishi Sunak na Birtaniya da Olaf Scholz shugaban gwamnatin JamusHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A wannan Laraba Firamnista Rishi Sunak na Birtaniya ke kawo ziyara ta farko zuwa birnin Berlin na Jamus tun lokacin da ya dauki madafun iko watanni 18 da suka gabata. Yayin zirayar Firaminista Sunak zai gana da Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz inda za su mayar da hankali kan hanyoyin taimakon Ukraine kare kanta da kuma yakin da ke faruwa a yankin Zirin Gaza na Falasdinu tsakanin kungiyar 'yan ta'adda ta Hamas da isra'ila.

Shekaru hudu da suka gabata Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar Tarayyar Turai, amma ta ci gaba da kasance kawar Jamus ta kut-da-kut  inda duk kasashe suke kungiyar tsaron NATO, da kungiyar G7 ta gaggan kasashe masu karfin arzikin masana'antu da kuma kungiyar G20 ta kasashen da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya.

Wannan ziyara ta firaministan Birtaniya tana zuwa kwana guda bayan majalisar dokokin kasarsa ta amince da wani shiri mai cike da cece-kuce na tisa 'yan gudun hijira da suka shiga kasar ta Birataniya ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Ruwanda da ke yankin nahiyar Afirka.