1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaminista Isra'ila ya fara ziyarar aiki a Kenya

Suleiman BabayoJuly 5, 2016

Gwamnatin Isra'ila ta yi alkawarin bunkasa dangantaka da kasashen nahiyar Afirka ta fannoni rayuwa dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/1JJV2
Kenia, Benjamin Netanjahu und Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters

Kasashen Kenya da Isra'ila sun yi alkawarin kara aiki tare wajen yaki da ta'addanci, kamar yadda Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana lokacin da ya fara ziyarar aiki a birnin Nairori fadar gwamnatin Kenya, cikin ziyarar da yake yi a kasashen Afirka.

Kasar ta Kenya ta kasance zango na biyu a ziyarar da Netanyahu ya fara daga ranar Litinin a birnin Kampala na Yuganda, albarkacin cika shekaru 40 da farmakin da Isra'ila ta kai filin jiragen sama kasar ta Yuganda inda ta ceci 'yan kasar da suke cikin jirgin saman Faransa na fasinja da wasu Falasdinawa suka yi garkuwa da mutanen.

Yayin wannan ziyara Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya nemi ganin kawo karshen sabanin da ake samu bisa dangantaka da Isra'ila, saboda tabbatar da ganin kawo ci-gaba da daina rayuwa a cikin tarihi na yaki da gaba. Kana shugabannin biyu na Kenya da Isra'ila sun yi tattaunawa kan harkokin tattalin arziki da aikin gona.