1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Mayar da mulki ga Abdallah Hamdok

Ramatu Garba Baba LMJ
November 21, 2021

Sojojin da suka kwace mulki a Sudan, sun mayar da ragamar mulki a hannun Firaminista Abdallah Hamdok bayan cimma wata yarjejeniya.

https://p.dw.com/p/43JJK
Sudan Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: AFP

Fadlallah Burma Nasir wanda shi ne shugaban jam'iyyar Umma ta Sudan din, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Hamdok zai kafa majalisar ministoci mai zaman kanta nan ba da jimawa ba. Hamdok ya ce ya amince da matakin ne domin kawo karshen zubar da jinin da ake yi a kasar, ya kuma ce za a sako duk wadanda ake tsare da su kan zarginsu da aka yi da adawa da sojojin da suka yi juyin mulki a tsawon lokacin da aka kwashe ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin.
Al'ummar kasar da dama dai sun ci gaba da zanga-zangar da aka shirya, inda suka doshi fadar gwamnati da ke Khartoum amma jami'an tsaron Sudan suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsasu. Tun dai a tsakiyar watan Satumbar wannan shekara da muke ciki ne, Hamdok ya fara fuskantar matsala bayan da masu adawa da gwamnatinsa suka toshe babbar tashar jiragen ruwa ta kasar, abin da ya haifar da karancin man fetur da kuma fulawa. An kuma samu karuwar rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kungiyar farrar hular da suka jagoranci kifar da gwamnatin Omar al-Bashir tare da nada Adallah Hamdok a matsayin firaminista a 2019. Wannan dai ya janyo juyin muilkin da sojoji suka yi a watan Oktobar da ya gabata, karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan.

Sudan Unruhen Proteste
Al'umma na ci gaba da zanga-zanga a SudanHoto: AFP