1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finland ta dauki matakin shiga NATO

Suleiman Babayo MAB
April 20, 2022

An tattaunawa a majalisar dokokin kasar Finland kan batun shigar kasar kungiyar tsaro ta NATO/OTAN, duk da adawa daga Rasha.

https://p.dw.com/p/4AAEg
DW l Finnland Russland l Zweiter Weltkrieg - Denkmal in Helsinki
Hoto: Teri Schultz/DW

A wannan Laraba majalisar dokokin kasar Finland ta bude muhawara kan shigar kasar kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN, sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine. Ita dai Finland tana cikin kasashen da ke makwabtaka da Rasha, kuma kasar ta Rasha ta sha nuna adawa kan shigar Finland kungiyar tsaron ta NATO.

A makon jiya Firaminista Sanna Marin ta ce cikin makonni masu zuwa kasar ta Finland za ta tantance matsayi kan shiga kungiyar ta NATO.

Kutsen da Rasha ta yi a Ukraine ya janyo muhawara kan shiga kungiyar NATO a kasashen na Finaland da Sweden, kana akwai gagarumin goyon bayan shiga kungiyar tsaron ta NATO a Finland, tun bayan kusten na Rasha a Ukraine.

A baya Finland ba ta shiga kungiyar NATO ba, saboda neman samun kekkyawar dangantaka da kasar Rasha, amma yakin da ke faruwa a Ukraine ya sauya komai.