1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Finland ya yi murabus

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 3, 2019

Takaddama tsakanin jam'iyyar 'yan gabadai-gabadai Social Democratic da kuma babbar jam'iyyar da ke cikin kawancen gwamnati ta masu matsakaicin ra'ayi Center Party a Finland, ta tilastawa firaminista yin murabus.

https://p.dw.com/p/3UAZg
Finnland Helsinki | Rücktritt Antti Rinne, Ministerpräsident
Firaministan Finland Antti Rinne da ya yi murabusHoto: Reuters/Lehtikuva/M. Stig

Murabus din Firaministan Antti Rinnena na Finland din dai, na zuwa ne watannin shida kacal bayan da ya kama aiki. Jam'iyyar kawancan ta masu matsakaicin ra'ayi wato Center Party ta bayyana cewa ta rasa karfin gwiwa a shugabancinsa. Hakan dai ya biyo bayan kwashe tsawon makonni biyu da ma'aikatan hukumar rarraba wasiku ta kasar suka yi suna yajin aiki. Halin da ake ciki a Helsinki dai na da matukar muhimmanci ga Turai, kasancewar Finland za ta ci gaba da rike shugabancin kungiyar Trayyar Turai na karba-karba har zuwa karshen wannan shekarar da muke ciki ta 2019.