1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Finidi ya ce kungiyar Super Eagles za ta dawo da martabarta

June 8, 2024

Babban mai horas da kungiyar kwallon kafa Super Eagles ta Najeriya Finidi George ya ce yana da yakinin cewar tawagarsa za ta dawo da martabarta a fagen kwallon kafa, a gasar cin kofin kwallon kafar duniya na 2026.

https://p.dw.com/p/4gooX
Babban mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya Finidi George
Babban mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya Finidi George Hoto: Nigerian National Football Federation

Goerge na wannan cika baki a bayan da Najeriya ta yi kunnen doki a wasan share fage da ta buda da kasar Afrika ta Kudu a birnin Uyo da ke kudancin kasar.

Karin bayani: Finidi ya zama sabon mai horar da Super Eagles

Najeriya ce ta biyar daga kasashen rukuni na uku wato Group C, inda take da maki 3 kacal a wasanni uku da ta buga, lamarin da ya sanya ta a wani hali na kila-wa-kala dangane da cancantar shiga gasar kwallon kafa ta duniya.A halin yanzu dai kasar Lesotho ce ke kan gaba a wannan rukunin da maki 5, inda ta dara kasashen Ruwanda da Benin da maki 1, yayin da kasar Afrika ta Kudu da za ta fuskanci Super Eagles a mataki na biyu ke da maki 4, sai kuma Zimbabwe da ke da maki 2.

Karin bayani: Cece-kuce kan raba gari da kochin Super Eagles Jose Peseiro 

Finidi George dai ya karbi ragamar kungiyar ta Super Eagles tun bayan rashin nasarar da Najeriyar ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka gudanar a kasar Côte d' Ivoire.