1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Filin jirgin saman Japan ya ci gaba da aiki

Abdullahi Tanko Bala
October 3, 2024

Jirage sun ci gaba da tashi a filin jirgin saman Japan bayan fashewar wani bam na zamanin yakin duniya na biyu jim kadan bayan saukar wani jirgi.

https://p.dw.com/p/4lNZj
Japan | Fashewar bam a filin jirgin sama na Miyazaki
Hoto: Kyodo/REUTERS

Filin jirgin saman Japan ya ci gaba da zirga zirgar jirage bayan tsayar da tashin jiragen na wani dan lokaci sakamakon fashewar wani bam da ke binne a karkashin kasa tun zamanin yakin duniya na biyu 'yan dakikoki kadan bayan da wani jirgin saman fasinja ya sauka a filin jirgin. Ba sami rahoton wani da ya ji rauni ba.

Fashewar bam din ya haifar da wagegen rami a titin jirgin

A wannan Alhamis ne dai aka bude filin jirgin na Miyazaki da ke kudancin Japan.

Jirage kimanin 80 aka soke tashin su a ranar laraba wanda ya shafi fasinjoji fiye da 3,400