1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA ta bukaci a mutunta al'adun Katar

Ramatu Garba Baba
November 7, 2022

Hukumar FIFA ta bukaci dukkanin tawagogin kasashe 32 da za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a Katar da su mutunta al'adun kasar.

https://p.dw.com/p/4J8mH
Magoya Kungiyar Dortmund na son a kauracewa gasar KatarHoto: Leon Kuegeler/REUTERS

Hukumar Kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta bukaci dukkanin tawagogin kasashe 32 da za su fafata a gasar cin kofin duniya, da su mayar da hankali kan abin da ya kai su kasar ta Katar, wanda shi ne kwallon kafa. Kiran na FIFA ya zo ne a daidai lokacin da ce-ce-ku-ce ya mamaye gasar da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamban da muke ciki, musamman game da cin zarafin dan adam da ake zargin kasar da aikatawa baya ga matakinta na haramta badala.

 Kasashen Turai da dama gami da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na caccakar Katar kan matsayinta na adawa da auren jinsi daya, da kuma yadda kasar ke take hakkin dan Adam, musamman akan mu'amala da ma'aikata bakin haure.

Rahotanni na cewa, akwai ‘yan wasan ma da suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana yayin da aka fara gasar ta cin kofin duniya don kalubalantar salon gwamnatin Katar na tauye hakkin dan adam a Paris, da sauran garuruwan Faransa, sun ce, ba za su nuna wasannin gasar cin kofin duniya a wuraren da jama'a ke taruwa a filaye ba, duk da cewa Faransa ce ke rike da kofin a yanzu.