1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA za ta bayyana wadanda za su kara a Katar

Abdourahamane Hassane
March 31, 2022

Hukumar wasannin  kwallon kafa ta duniya  FIFA ta soma gudanar da taronta na shekara shekara  a birnin Doha na Katar.

https://p.dw.com/p/49J0C
Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni Infantino Hoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

Taron wanda shi ne karo na 72, na cike da rarrabuwar kawuna a game da sabbin dokoki da hukumar ke son aiwatarwa, wadanda suka hada da dawo da gasar cin kofin duniyar na kwallon kafa  a tsawon shekaru biyu a maimakon hudu, da kuma wasu sauye-sauyen a fanin gasar wasannin klub-klub. A gobe juma'a aka shirya hukumar za ta bayyana rukunin-rukuni na kasashen da zan su kara a zagaye na farko na gasar ta Katar bayan an yi wala-wala.