1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗuwr Euro na da tasiri a kasashen duniya

October 6, 2011

Masana harkar tattalin arziki sun gargadi kasashe masu tasowa da su dau mataki na kare tattalin arzikinsu, domin faduwar darajar takardar Euro zai shafi kasashe masu tasowa, ganin yadda suka dogara da hajar Turai

https://p.dw.com/p/12nLe
Kwadololin EuroHoto: picture alliance/dpa

Matsalolin tattalin arzikin da ke fuskantar takardar kudin Euro sakamakon matsalar da ya afkawa tattalin arzikin kasar Girka na ci gaba da zama abin damuwa ga kasashe da dama saboda tsoron yadda lamarin ka iya shafar tattalin arzikin duniya.

Wannan matsalar da ke kalubalantar takardar kudin ta Euro da ta faro daga matsalar tattalin arzikin da ta afkawa kasar Girka wacce kasashen Turai suka yi ta kai mata dauki, to sai dai sannu a hankali matsalar na zama wutar daji da a yanzu ke kalubalantar kasashen Italiya da Spaniya da ma Portugal.

Ford Autos werden mit Barco Ford verschifft
Motoci dake kan hanyar zuwa AfrikaHoto: AP

Bazuwar matsalar da ma yadda take kara yin kamari a dai dai lokacin da tattalin arzikin duniya baki daya ke fuskantar sabon kalubalen koma baya ya sanya takardar kudin tarayya watau Euro fusknatar babban kalubale saboda tasirin da dimbin bashin da ke kan wasu kasashen Turai da ke da shi.

Duk da cewa ana wa wannan matsalar kallon ta shafi kasashen Turai ne da ke amfani da takardar kudin Euro, to sai dai ga kasashe Afrika irin Najeriya da ba wai kai tsaye sun dogara a kan takaradar kudin Euron bane wannan matsala na iya shafar tattalin arzikinsu. Kamar yadda Malam Ahmed Rabiu kwararre a kan harkokin zuba jari na kasa da kasa da ke Najeriya ya bayyana.

MC Lagos Marktfrau
Wata yar kasuwa a LagosHoto: DW

Kwararru a fanin harkokin tattalin arziki na masu bayyana tsoron cewar koma bayan da ake tsoron matsalar takardar kudin Euron za ta haifar ga tattalin arzikin duniya zai iya shafar yan kasuwar Najeriyar, saboda yadda tattalin arzikin ya kasance mai dogaro da shigo da kaya daga kasashen duniya ciki hard a kasashen Turai.

To sai dai a dai-dai lokacin da kasashen Turai suka dukufa wajen nemo hanyar shawo kan wannan matsalar ta hanyar talafawa kasashen da dimbin bashin da suka afka cikinsa ke girgiza matsayin takardar Euro ya sanya tambayar shin wane mataki ya kamata Najeriya ta dauki matakan riga kafi, inji Malam Ahmed Rabiu kwararren masani harkar zuba jari na kasa da kasa.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da wannan matsalar za ta iya yin tasiri sosai a cikinsu, domin kuwa baya ga barazanar da takaradr Euron ke fiskanta ga faduwar farashin mai da ke shafar tattalin arzikin Najeriyar abon dogaro da ta yi a kansa domin samun mafi yawan kudin shigarta, lamarin day a sanya gwamnatin fara kama hanyar sake fasalin kasafin kudinta da ma hasashen yiwuwar rage darajar takardar kudin kasar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Usman Shehu Usman