1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗuwar darajar takardar kuɗin bai ɗaya ta Euro

September 13, 2011

Amurka ta shawarci Turai da ta gyara manufofin ta na kuɗi da tattalin arziƙi.

https://p.dw.com/p/12YBV
Hoto: picture-alliance/dpa/DW

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi kira ga shugabannin nahiyar Turai da su ƙara himma wajen ciyo kan matsalar bashin da ke addabar ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin bai ɗaya na Euro. A wata hira da ya yi da wakilan kafofin yaɗa labarai a Fadarsa ta White House, Obama ya ce a yanayi irin wannan da matsalolin tattalin arziƙin duniya ke zama bai ɗaya, matsalolin ƙasashen da ke amfani da takardun kuɗin euro yana tasiri sosai a Amurka.

Ya kuma ƙara da cewa wajibi ne shugabanin yankin su yanke shawarar yadda zasu yi kwaskwarima a manufofin da suka shafi kasafin kuɗi da tattalin arziƙin ƙasashen su. Gwamnatin ta Obama a yanzu, tana aiki tare da shugabanin na Turai domin shawo kan rikicin kuɗin Girka da sauran ƙasashen da ke fama da durƙushewar tattalin arziƙi. Ranar juma'a mai zuwa ake sa ran sakataren baitalmalin Amurka Timothy Geithner zai halarci wani taron Ministocin kuɗin Turai wanda za'a ƙaddamar a kasar Poland.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita Abdullahi Tanko Bala