1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗar ƙabilanci ya bazu a Sudan ta kudu

January 3, 2012

Dubban jama'ane suka bar gidajensu, bayan ɓarkewar tashin hankali da ya shafi ƙabilanci a kan mallakar filaye a kasar Sudan ta kudu

https://p.dw.com/p/13dLd
Mehr als 100 Tote bei Stammeskämpfen im Südsudan ARCHIV - Einwohner von Duk Padiet im Südsudan bewachen am 22.09.2009 ihren Ort, nachdem dieser zwei Tage zuvor überfallen worden war. Der 9. Januar 2005 war für viele Menschen im Sudan mit großen Hoffnungen verbunden: Mit der Unterzeichnung des Friedensabkommens zwischen Nord und Süd wurde der Schlusspunkt unter einen der längsten Konflikte des Kontinents gesetzt. Zwei Jahrzehnte lang hatten der überwiegend von arabischstämmigen Moslems bewohnte Norden und der von schwarzafrikanischen Christen und Animisten bewohnte Süden einen erbitterten Bürgerkrieg geführt. Die Bevölkerung des Südsudans fühlte sich politisch und wirtschaftlich vom Norden benachteiligt. Nach dem Tod von etwa zwei Millionen Millionen Menschen und der Flucht und Vertreibung von vier Millionen Sudanesen vor allem im durch den Krieg schwer zerstörten Süden sollte das Land endlich zur Stabilität zurückkehren, mit einer Teilautonomie des
Wasu mayaka dauke da bindiga a kasar Sudan ta kuduHoto: picture alliance / dpa

Rahottani daga Sudan ta kudu na cewa dubun-dubatan jama'a na ta ficewa domin gujewa rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a wasu ƙauyuka dake yankin na sabuwar ƙasar Sudan ta kudu. Majiyoyi daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce 'yan bindiga kimanin 6,000 daga kabilar Lau Nuer suka afkawa garin Pibor sakamakon ɗauki ba daɗi da 'yan ƙabilar Murle. Majalisar Ɗinkin Duniyar ta kiyasta cewa an kashe mutane 1,000 tun bayan da rikicin ya ɓarke. Ƙungiyar agajin likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta dakatar da ayyuka a yankin bayan da mayaƙan suka lalata wasu asibitocinta biyu a sakamakon faɗan. An ruwaito cewa gwamnatin kudancin Sudan ɗin da Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin tura ƙarin jami'an tsaro domin samar da zaman lafiya a yankin.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita:        Usman Shehu Usman