1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na tir da mamayar Rasha a Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 13, 2022

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi ba bisa ka'ida ba a yankunan Luhansk da Donetsk da Zaporizhia da Cherson da ke gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4I762
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi wa yankunan Ukrain
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi wa yankunan UkrainHoto: Bebeto Matthews/AP/dpa/picture alliance

Kasashe 143 daga cikin kasashe 193 na duniya sun kada kuri'ar amincewa da kudurin yin tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, yayin da kasashe 35 suka ki amincewa da shi ciki har da Rasha da Siriya da Nicaragua da Koriya ta Arewa da Belarus.

Bisa ga dokokin kasa da kasa dai ba dole ba ne a aiwatar da kudirin, amma ya nuna yadda Moscow ke zama saniyar ware a duniya. Har ila yau kudurin ya sake tabbatar da 'yancin kai da walwala na Ukraine a kan iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.