1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar bam ya janyo mutuwar mutane 5 a Siriya

May 22, 2012

Gwamnatin Siriya ta zargi 'yan adawar ƙasar ta tarwatsa bam a wani gidan sayar da abinci.

https://p.dw.com/p/14zi0
Mourners carry the coffins of victims, who was killed in Thursday's suicide bomb attack, during a funeral official at al-Othman mosque in Damascus May 12, 2012. Two suicide car bombers killed 55 people and wounded 372 in Damascus on Thursday, state media said, the deadliest attacks in the Syrian capital since an uprising against President Bashar al-Assad began 14 months ago. REUTERS/Khaled al-Hariri (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS MILITARY)
Hoto: Reuters

Mutane biyar ne suka mutu - a wannan Talatar, sakamakon fashewar wani abu a wani gidan sayar da abinci dake yankin Qaboun a wajen Damascus, babban birnin ƙasar Siriya. Kafofin yaɗa labaran gwamnati da kuma ƙungiyar kare haƙƙin jama'a ta ƙasar Siriya wadda cibiyar ta ke birnin London na Birtaniya ne suka sanar da hakan. Qaboun, wanda ke arewacin birnin na Damascus ya kasance cibiyar gudanar da jerin zanga zangar neman kawo ƙarshen mulkin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ta Siriya, kuma yankin yayi ta fama da fito na fito a tsakanin magoya bayan shugaban na Siriya da kuma masu adawa da mulkin sa.

Tashar telebijin ta ƙasar Siriya ta ɗora alhakin tashin bam ɗin akan waɗanda ta ƙira 'yan "Ta'adda" kalmar da hukumomin Siriya ke yin anfani da ita akan masu adawa da ita. Hukumomin Siriya dai sun taƙaita baiwa kafofin yaɗa labarai damar shiga cikin ƙasar tun bayan ɓarkewar boren neman kifar da gwamnatin shugaba Assad kimanin watanni 14 da suka gabata, wanda a yanzu ya rikiɗa zuwa ɗaukar makamai daga ɓangaren bijararrun sojoji, abinda kuma yasa da wahala a tantance sahihancin rahotanin dake fitowa daga can.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe