1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin jiragen NATO akan gidan Gaddafi

April 25, 2011

NATO ta yi luguden wuta da jiragen sama akan rukunin gidajen Gaddafi wanda ya haɗa da ofishinsa a Tripoli

https://p.dw.com/p/113RF
Sojin Libya yayinda suke duba ɓarnar harin NATO ga rukunin gidajen Gaddafi a birnin TripoliHoto: dapd

A ƙasar Libya da sanyin safiyar yau an jiwo fashewar manyan bama bamai mafi girma a tsawon makonni a tsakiyar Tripoli babban birnin ƙasar. Farmakin wanda dakarun ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ta kai a yau Litinin ya lalata ginin da shugaba Gaddafi yake ciki. An kuma ruwaito cewa an ji fashewar bama bamai a wasu gundumomi a birnin na Tripoli yayinda NATO ke cigaba da farmaki da jiragen sama. Wani jami'in gwamnatin Libyan yace kimanin mutane 45 sun rasu yayinda wasu goma sha biyar kuma suka sami munanan raunuka. Harin dai ya zo ne kwana guda bayan da sojojin Gaddafi suka yi luguden wuta da rokoki akan yankin tashar jirgin ruwa dake Misrata wanda ya yi hasarar rayukan mutane da dama.

A halin da ake ciki Ministan harkokin wajen Libyan Abdelati Obeidi na kan hanyar zuwa ƙasar Habasha domin tattauna shirin zaman lafiya wanda ƙungiyar gamaiyar Afirka ta gabatarwa Gaddafi a wannan watan. Gwamnatin Libyan dai ta amince da shirin samar da zaman lafiyar amma 'yan tawaye sun yi fatali da shi suna mai cewa dukkan wani shirin zaman lafiya dole ne ya ƙunshi buƙatar Gaddafi ya sauka daga karagar mulki.

A hannun guda ƙasashen Amirka da Birtaniya da Faransa sun ce ba za su sassauta da farmakin da suke kaiwa da jiragen sama ba, har sai Gaddafi ya yi murabus. Da yake tsokaci dan Majalisar dattijan Amirka na Jam'iyyar Republican Sanata John McCain ya yi bayani da cewa " A halin da ake ciki mutanen nan kan su a haɗe yake sun ƙosa da mulkin Gaddafi, sun haɗa kai kamar yadda yake faruwa a Tunisia da Masar da Syria da kuma sauran ƙasashe suna neman yanci. Ba Alƙa'ida ce ta assasa wannan tarzoma ba, buƙata ce ta jama'a waɗanda ke neman 'yancinsu da kuma cigaban dimokraɗiyya".

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi