1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake baiyanar COVID-19 a Chaina

Zainab Mohammed Abubakar
June 13, 2020

Mahukuntan kasar Chaina sun dauki matakan kwarya-kwaryar rufe wasu yankuna a Beijing saboda sake bullar COVID-19 da gudun yaduwarta.

https://p.dw.com/p/3diHO
China Peking Abriegelung Xinfadi Markt
Hoto: picture-alliance/STR

Rahotanni daga kasar Chaina na nuni da cewar, gomman mutane da ke aiki a wata babbar kasuwa sun kamu da kwayar cutar corona. An tabbatar da cutar a jikin mutane 45 daga cikin 'yan kasuwa 517 da aka yi wa gwaji a babbar kasuwar ta Xinfadi da aka rufeta.

Tuni dai mahukuntan kasar suka sanar da killace yankuna goma sha daya da ke kewayen kasuwar ta sarin kaya, da wasu kasuwanni da ke wannan birni, na wucin gadi.

Kazalika, wani gwaji da aka yi a kasuwar 'yan gwari na nuni da cewar, a nan ma wasu sun kamu. Matakin rufe kasuwannin ya biyo bayan samun sabbin mutane hudu ne da suka harbu da Covid-19, wadanda suka yi ma'amala da mutane a kasuwar da ke gunduwar Fengtai.