1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farfado da tattaunawar tsagaita wuta a Yemen

February 3, 2019

Wakilan gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a Yemen da kuma yan tawayen Houthi sun gana a tashar gabar ruwan Hodeida a yau Lahadi domin farfado da tattaunawar tsagaita wuta a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3CeeT
Jemen Houthi-Kämpfer unterstützen Friedensgespräche
Hoto: picture alliance/AP Photo/H. Mohammed

Bangarorin biyu dai a tattaunawar da suka yi a watan Disamba a kasar Sweden sun amince da janye mayakansu daga muhimman wurare a birnin na Hodeida da kuma bude kofar kai kayan agaji a ranar 7 ga watan Janairu. To amma tun daga wannan lokaci kokarin aiwatar da yarjejeniyar ya ci tura.

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ke shiga tsakani domin warware rikicin da aka shafe shekaru hudu ana yi da kuma kokarin kaucewa ta'azzarar rikicin a Hodeida.