1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman makisan shugaban Haiti ruwa a jallo

Abdul-raheem Hassan
July 8, 2021

Hukumomin tsaro a kasar Haiti na cigaba da farautar mutanen da ke da hannu a kashe Shugaban kasar Jovenel Moise bayan bude masa wuta da bindiga a jiya Laraba.

https://p.dw.com/p/3wDwd
Haiti | Ermordung Präsident Jovenel Moise
Hoto: Valerie AFP/Getty Images

Tsananta binciken ya biyo bayan kashe wasu mutum hudu, tare da kama wasu biyu, 'yan sanda sun kuma ja kunnen duk wani mai hannu a kisan gillar da ya gaggauta mika kansa ga hukuma.

Kasashen duniya sun yi tir da kisan da ya jefa al'ummar kasar cikin rudani, yayin da masana harkokin tsaro ke fargabar makomar kasar da ta sha fama da tashe-tashen hankula a shekarun baya. Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na makonni biyu don nuna alhinin mutuwar Shugaba Moise mai shekaru 53.