1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukuntan Beljiyam na farautar maharan Paris

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 23, 2015

'Yan sandan kasar Beljiyam na ci gaba da samame a birnin Brussels, a kokarin da suke na kamo wadanda ake zargi da hannu a kitsa harin ta'addancin da aka kai birnin Paris na Faransa.

https://p.dw.com/p/1HAsI
Farautar maharan Paris a birnin Brussels na kasar Beljiyam
Farautar maharan Paris a birnin Brussels na kasar BeljiyamHoto: picture-alliance/dpa/S. Lecocq

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan sandan sun sake cafke wasu mutane biyar yayin da suka tsare da wasu 16, inda kuma birnin ke ci gaba da zama cikin dokar ba shiga ba fita, a kokarin da suke na farautar wadanda ake zargi da harin na Paris ciki kuwa har da na kan gaba a zargin wato Salah Abdeslam. A hannu guda kuma Firaministan Birtaniya David Cameron ya shaidawa shugaban kasar Faransa Francois Holland cewa zai nemi amincewar majalisar dokokin Birtaniyan domin shiga a dama da kasarsa a hare-haren taron dangi da jiragen yaki ke kai wa a kan 'yan ta'addan IS a Siriya. Harin na birnin Paris dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 130, yayin da wasu da dama suka jikkata.