1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farashin danyan mai ya yi tashin gwauron zabi

June 1, 2021

Farashin danyan man fetur ya yi tashin gwauron zabi a kasuawannin duniya, sa'oi kalilan gabanin fara taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.

https://p.dw.com/p/3uFhe
Symbolbild OPEC, Organisation Erdöl exportierender Länder
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Gindl

A wajen taron na wata-wata, ana sa ran kasashen masu arzikin na man fetur za su tattauna batun kara yawan gangunan danyan man da suke fitarwa, duba da cewa tattalin arzikin kasashen duniya ya fara farfadowa daga tu'annatin da annobar Corona ta yi masa.

Lamarin da ake danganta shi da nasarar da ake samu wajen gudanar da alluran rigakafin COVID-19, musamman a kasashe masu karfin tattalin arziki da suka hada da Amirka da kasashen nahiyar Turai.