1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula sun salwanta a harin ta'addanci a Nijar

July 18, 2024

Sojoji a Nijar sun bayyana yadda wasu mahara suka halaka wasu fararen hula a wani kauye da ke a yammacin yankin Tillaberi mai fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

https://p.dw.com/p/4iRkT
Soja a Jamhuriyar Nijar
Jami'in soja da makaminsa a Jamhuriyar NijarHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Akalla fararen hula mutum bakwai hukumomin soja a Nijar suka tabbatar da cewa 'yan ta'adda suka kashe cikin wannan makon a wani hari da suka kai kansu a Dosso Kouregou.

Maharan a cewar sojoji a Nijar, sun kuma sace dabbobi musamman shanu, sai dai ba su fadi ranakun da abin ya faru a cikinsu ba.

Sojojin sun kuma ce ana ci gaba da bincike, domin tsefe batun da kyau tare da hukunta wadanda suka aikata.

Kafin shi wannan harin na kauyen Dosso Kouregou ma dai, sojojin sun ce kashe wasu 'yan ta'adda mutum 13 tare da kama wasu 29 a yankin.

Dosso Kouregoun dai na kusa da Kokoru ne da ke a yammacin Tillaberi, yankin da mahara suka kashe sojoji 20 a cikinsa a ranar 25 ga watan jiya.