1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani kan makomar Jamhuriyar Nijar

Suleiman Babayo USU
August 1, 2023

Gwamnatocin mulkin sojan kasashen Burkina Faso da Mali sun yi gargadi kan matakin sojan kan Jamhuriyar Nijar, yayin da wa'adin da kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin ke karatowa.

https://p.dw.com/p/4UcgS
Coup aftermath in Niger
Dama: Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/REUTERS

Gwamnatocin mulkin sojan kasashen Burkina Faso da Mali sun yi gargadi kan duk wani matakin sojan kan Jamhuriyar Nijar, domin yunkurin mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan madafun iko. Kasashen na Burkina Faso da Mali sun ce duk wani hari kan Jamhuriýar Nijar zai zama matakin kaddamar da yaki kan kasashen ne.

Sanarwanar tana zuwa bayan kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS da goyon bayan kasashen duniya sun dankara takunkumin kan gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da barazanar amfani da karfi muddun sojoji suka ci gaba da rike madafun ikon kasar. Haka ita gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea ta cire irin wannan sanarwar goyon baya ga sojojin da suke rike da ragamar tafiyar da Jamhuriyar Nijar.

A wani labarin sojojin da suka yi juyin mulkin a Jamhuriyar Nijar suna ci gaba da kame mambobin tsohuwar gwamnatin farar hula da suka kifar inda Janar Abdourahmane Tchiani ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar ta Nijar. Tuni kasashen Faransa da Italiya suka bayyana shirin kwashe 'yan kasarsu daga Jamhuriyar ta Nijar mai fama da rudanin siyasa bayan juyin mulkin.