1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta musanta raunata farar hula a Burkina Faso

November 22, 2021

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce dai masu zanga-zangar suka datse hanyar da sojojin Faransa ke bi zuwa Jamhuriyar Nijar a daidai wani gari da ake kira ''Kaya'' da ke Burkina Faso. 

https://p.dw.com/p/43Lgm
UN-Minusma Mali-Mission | Französische Truppen
Hoto: Speich Frédéric/Maxppp/dpa/picture alliance

Rahotanni sun ce sojojin na Faransa sun yi harbe-harbe a iska da harsashen roba don tarwatsa masu zanga-zangar. Sai dai daga bisani aka zarge su da harbin mutane da harsashi na gaskiya. To amma a wannan Litinin Pascal Lanni da ke magana da yawun sojojin na Faransa a Burkina Faso ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa bincikensu ya nuna sojojin ba su ji wa kowa rauni ba.

Mutanen Burkina Faso dai sun fusata ne da yadda suke zargin sojojin na Faransa da kasa tsare su a yayin da suke ci gaba da zama a kasar da sunan samar da tsaro.