1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Faransa sun halaka dan IS a Nijar

December 21, 2021

Sanarwar da sojojin Faransar suka fitar ta ce tun a shekara ta 2021 lokacin da IS ta kai wa Faransawa hari a Nijar aka tura wasu sojoji na musamman kan iyakar Nijar da Burkina Faso da Mali domin su gano 'yan ta'addar. 

https://p.dw.com/p/44den
Mali Französische Soldaten
Hoto: Daphné Benoit/AFP/Getty Images

Sojojin Faransa sun sanar a wannan Talata cewa sun yi nasarar kashe daya daga cikin 'yan ta'addar IS da suka kai wa ma'aikatan agaji na Faransa da ke aiki a Jamhuriyar Nijar hari a shekarar da ta gabata. 


Faransawan sun ce a ranar Litinin ne dai sojojin nasu hadin gwiwa da na Nijar suka bindige dan ta'addar a wani hari ta sama bayan da aka samu labarin cewa yana cikin wadanda suka halaka Faransawa a bara.


'Yan kungiyar ta IS dai sun halaka Faransawa shida da wasu 'yan Nijar biyu a lokacin da suka kai hari kan ma'aikatan agajin na Faransa a shekarar da ta wuce. A watan Agustar da ya gabata sojojin Faransan sun ce sun bindige jagoran mayakan IS da suka kitsa harin.