1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na zargin sojin Nijar na garkuwa da jakadanta

September 16, 2023

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewa sojojin Nijar sun yi garkuwa da jakadan kasar Sylvain Itte lamarin da ke hana masa samun isashen abinci da kayan more rayuwa ba.

https://p.dw.com/p/4WPge
Faransa na zargin sojojin Nijar da yin garkuwa da jakadantaHoto: Hugo Ortuño/picture alliance/dpa/EPA

Macron ya ce sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimokuradiyya ta Nijar sun toshe duk wasu hanyoyi na kai wa jakadan da abokan aikinsa abinci, lamarin da ya tilasta masa dogara da abincin da sojojin Faransa da ke girke a kasar ke ci.

Karin bayani: Nijar ta umarci yan sanda su fitar da Jakadan Faransa

A karshen watan Ogustan da ya gabata ne dai sabbin jagororin sojan Nijar karkashin Birgediya Janar Abdourahamane Tiani suka bukaci jakadan da ya tattara komatsensa ya fice daga kasar, matakin da Faransa ta ce ba za ta mutumta ba domin sojojin ba halastattun shugabanni ba ne.

Karin bayani: Nijar ta umurci fitar da jakadan Faransa daga kasar

Ministar harkokin wajen Faransar Catherine Colonna ta jaddada cewar jakadan zai ci gaba da zama a Nijar muddin shugaba Macron na kan bakansa, sannan kuma har yanzu hambararren shugaba Mohamed Bazoum shine halastaccen shugaban Nijar.

Karin bayani: Faransa ta ce jakadanta na nan daram a Nijar