1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na shiri kan 'yan gudun hijira

Yusuf BalaJune 17, 2015

Gwamnatin Faransar dai ta amince da samar da gidaje 5,000 ga wadanda aka basu mafakar siyasa a kasar, sannan za ta gina wasu gidajen 4,000 ga wadanda ke neman mafakar ta siyasa.

https://p.dw.com/p/1Fif7
EU-Staaten Streit um Flüchtlingsfrage
Hoto: picture-alliance/dpa/MOAS.EU/ Darrin Zammit Lupi


A ranar Laraban nan kasar Faransa ta bayyana shirin samar da karin gidaje 10,500 don tarbar 'yan gudgun hijira da ke kwarara zuwa kasashen Turai bayan tsallaka tekun Bahar Rum.

Gwamnatin kasar ta Faransa dai ta amince da samar da gidaje 5,000 ga wadanda aka basu mafakar siyasa a Faransa, sannan za ta gina wasu gidajen 4,000 ga wadanda ke neman mafakar ta siyasa, kana za a samar da wasu gidaje 1,500 da za su zauna cikin shirin ko ta kwana ga wadanda ke shiga Turai ta barauniyar hanya.

Cikin shekaru bakwai dai da suka gabata mutanen da ke zuwa Faransa da zummar neman mafakar siyasa sun ninka adadin da ake da su na 66,000 a shekarar 2013.

Saboda dai karancin na muhalli a yanzu ya sanya masu neman mafakar siyasar na kwana a wurare marasa inganci.