Faransa na rufe sansanin Calais
October 24, 2016A yanzu dai an girke jami'an tsaro kusan 1,250 da manyan motoci da za su kwashe bakin haure kusan dubu 8,000 izuwa sassa daban daban na kasar ta Faransa. To sai dai wasu daga cikin mazauna sansanin na Calais na ganin matakin da gwamnati ta dauka na murkushe mazaunin da suka shafe sama da shekara guda a matsayin rashin tausayi da jinkai. Mafi akasarin mazauna sansanin dai 'yan kasashen Afganistan ne da kuma Iritiriya da 'yan kasar Sudan da ke da niyar ketarawa nahiyar Turai.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumomin Faransa ke yunkurin rufe sansanin ba, amma 'yan gudun hijiran ke sake tarewa a ciki. Wannan karon dai gwamnatin Faransa ta dau matakin rufe sansanin na Calais ne har abada da nufin samun saukin tashin tashina tsakanin jami'an 'yan sanda da bakin hauren da ke makalewa man'yan motoci dan tsallakwa zuwa Turai.