1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Faransa na ziyara a Aljeriya

Abdoulaye Mamane Amadou Sulaiman Babayo
October 9, 2022

Firaminista Elisabeth Borne ta jagoranci wata tawagar ministocin Faransa zuwa Aljeriya a kokarin da kasashen biyu ke yi na dinke baraka da karfafa huldar kasuwanci

https://p.dw.com/p/4HxMe
Algerien Frankreich Emmanuel Macron und Abdelmadjid Tebboune
Hoto: Ludovic Marin/AP/picture alliance

Wata tawagar gwamnatin Faransa karkashin jagorancin firaminista Elisabeth Borne na ziyarar aiki a Aljeriya, a kokarin gwamnatin Shugaba Macron na bankwana da barakar da ta taba kunno kai a tsakanin kasashen byiu ta hanyar diflomasiyya da bunkasa tattalin arziki. 

Wasu daga cikin muhimman batutuwan da suka kai tawagar a Aljeriya har da batun makamashi baya ga huldar kasuwanci, kana shugabar gwamnati Borne da ke samun rakiyar ministoci 16 za ta gana da Shugaba Tebboune a wannan Litinin.