1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta halaka shugabanin IS

Ramatu Garba Baba
July 23, 2021

Faransa ta ce tayi nasarar halaka wasu manyan shugabanin Kungiyar IS da suka yi kaurin suna a yada manufarsu a kasashen yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3xxfr
Syrien Angriff auf IS Stellungen in Baghouz
Hoto: Getty Images/AFP/G. Cacace

Ma'aikatar tsaron Faransa ce ta fitar da sanarwar nasarar halaka shugabanin Kungiyar IS a yayin wani samame da suka kai kan mabuyarsu da ke Menaka. Samamen da Faransan ta kai da taimakon rundunar sojin Amirka, ya halaka Abu Abderahman al-Sahraoui da mataimakinsa Issa al-Sahraoui.

Ma'aikatar tsaron Faransan, ta kara jadada fata na ganin bayan mayakan masu da'awar jihadin, ta ce wannan nasarar, ta nuna jajircewa kasar a yakar 'yan ta'adda duk kuwa da shirin kasar na rage yawan sojojin da ta jibge a yankin Sahel, bayan da ta kwashe fiye da shekaru takwas tana fada da masu tayar da kayar bayan.