1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Jibouti sun sake tsawaita yarjejeniyar tsaro

July 25, 2024

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da kuma takwaransa na Jibouti Omar Guelleh sun amince da sake tsawaita yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4ii2M
Shugaban kasar Jibouti, Omar Guelleh
Shugaban kasar Jibouti, Omar GuellehHoto: Mohammed Dhaysane/AA/picture alliance

Kasashen Faransa da Jibouti sun sake cimma yarjejeniyar tsaro bayan kwashe shekaru biyu ana kai komo. A cewar wata majiya da ke kusa da masu tattaunawa, an samu jinkiri ne sakamakon bukatar Jibouti na neman Faransa ta kara kudin hayan da take biya domin girke sojojinta.

A cikin sanar da fadar shugaban kasar Faransa ta fitar, ta ce yarjejeniyar da aka saka hannu a kanta a offishin Shugaba Macron, na kunshe ne da kasancewar dakarun Faransa 1,500 a karamar kasar da ke gabashin Afirka. Tun dai a shekarar 1977 ne aka fara sanya hannu kan wannan yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro tsakanin kasar Jibuti da uwargjiyarta Faransa tare da sabunta ta a shekarar 2011.