Faransa da Jamus na son ciyar da Turai gaba
September 7, 2018Talla
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za su tattauna kan tsare-tsaren 'yan gudun hijira da sauye-sauye kan harkokin kasashen da ke Turai da huldodin kasashen na Turai da wasu kasashe irinsu Siriya da Ukraine da kasashen yankin Balkans. Mai magana da yawun shugabar gwamnatin ta Jamus ya bayyana haka a wannan Juma'a.
Macron da Merkel na da buri na samun daidaito a tataunawarsu a birnin Marseille a kokarin da suke na ganin sun hada kai wajen ciyar da kasashen Turai gaba kamar yadda Steffen Seibert mai magana da yawun Merkel ya bayyana.