1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta lamshe mujami'ar Notre-Dame a Faransa

Usman Shehu Usman AMA
April 16, 2019

Hukumomi a kasar Faransa sun fara binciken musabbabin gobarar da ta tashi a mujami'ar Note Dame mafi suna kuma ta kasance daya daga cikin wuraren da suka fi muhimmanci ga Faransawa.

https://p.dw.com/p/3Gtpw
Frankreich Brand Notre Dame
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M. Stoupak

Mujami'ar Notre-Dame an kafa ta ne tun kimanin shekaru 850 da suka gabata, kuma an yi kiyasin mutane miliyan 14 ke kai ziyara a wannan mujami'ar don yawon bude ido. Hakan ya sa mujami'ar ta kasance wata babbar alama ga kasar Faransa ta hanyar samun kudi ga 'yan kasuwa wasu dalilin da suka sa tashin gobarar ke bayyana zaman makoki a kasar ta Faransa.

Mujami'ar Notre-Dame ta kasance abin alfahari ga Faransawa, sannan kuma ko baya ga Faransawan da akasari Kiristoci ne akwai wasu hidindimu da suka shafi shugabannin kasa duk a wannan mujami'a ake yinsa inji dan jarida Saddiq Abba mazaunin birnin Paris.

Ko da yake har yanzu babu tabbacin abin da ya jawo tashin gobara wacce shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kwatanta da cewa wani bala'i, a yanzu dai hankali ya koma kan batun sake gina wannan katafaren mujami'a wadda aka kafa tun shekaru 850 da suka wuce.

Kamfanoni da sauran jama'a sun ware Euro miliyan 500 don sake gina Notre-Dame, abin da ke nuna cewa za a iya samun miliyoyin kudi don sake ginin. Sai dai kasancewar tsohon gini ne dole ana bukatar kwararru da za su iya mayar da ginin ya yi daidai da wadda gobabar ta lalata.