1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutikar kare dabbobi a Katsina

December 14, 2016

A jihar ta Katsina Arewa maso Yammacin Najeriya an samu wani da ya tashi tsaye wajen ganin ba a ciwa dabbobi zarafi ba, inda ya ke leka mayanka da zama da makiyaya.

https://p.dw.com/p/2UH2I
Indien Jaipur - Cattle fair India 2016
Hoto: DW/J. Sehgal

Wani mai fafutukar kare hakkin dabbobi a jihar Katsina ya kafa wata kunguya da ke yaki da cuta wa dabbobi inda ya ke fadakar da al'umma yadda ya kamata su ruka kulawa da dabbobinsu a matsayin dukiyar da Allah ya ba su walau 'yan kasuwa ko kuma masu kiwo.

Shidai wannan mai kare hakkin dabbobi Abu Dan Malan Karofi ya kan shiga kasuwannin siyar da dabbobi da yin taruka da makiyaya gami da shiga kafafen yada labaru ya na fadakar da jama'a kan illar cutar da dabbobi dan haka ya kafa kungiyar kare dabbobin.

Vogelnest Mutter Küken
Hoto: picture-alliance/All Canada Photos

"Na kafane saboda ina da sha'awar na ga dabbobi da tsintsaye duk an ba su hakkinsu ina kokarin na ga cewa na kyautata masu rayuwarsu yadda kowa ke jin dadi a duniya, da kuma makomata a lahira saboda so nake ko na mutu 'ya'yana su cigaba saboda sadakatur jariya".

A cewar Abu Dan Malam akwai doka da aka tanada dan kare dabbobi a Najeriya sai dai ba ta da karfi dan haka ya ke fata a tsananta dokar. Dabbobi dai halitune da ke jure dukkanin abun da me kula da su ke masu saboda ba su da bakin da zasu iya kai kara gaban mahukunta.