1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Turai ta yi gargadi kan masu matsanancin ra'ayin Isra'ila

Suleiman Babayo USU
December 13, 2023

Shugabar Tarayyar Turai ta nuna damuwa game da masu matsananci ra'ayi na Isra'ila da ke kai hare-hare kan Falasdinawa a yankin gabar yamma da kogin Jodan, abin da ke tarnaki bisa samun zaman lafiya tsakanin bangarorin.

https://p.dw.com/p/4a7Qv
Ursula von der Leyen shugabar hukumar Tarayyar Turai
Ursula von der Leyen shugabar hukumar Tarayyar TuraiHoto: Christophe Licoppe/EU

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen a wannan Laraba ta bayyana goyon bayan saka takunkumi kan masu matsanancin ra'ayi 'yan Isra'ila da suke matsunan 'yan kaka-gida suke kai hare-hare kan Palasdinawa a yankin gabar yamma da kogin Jodan. Babbar jami'ar ta tarayyar Turai ta ce irin wannan hare-hare suna tarnaki kan neman samun zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu na Isra'ila da Palasdinu. Ita dai Ursula von der Leyen ta bayyana haka ga 'yan majalisar dokokin tatayyar Turai.

Shi ma Shugaba joe Biden na Amirka ya gargadi Isra'ila cewa za ta iya rasa goyon bayan da take samu na kasashen dunyia kan yakin da take yi da tsagerun kungiyar Hamas muddun ta ci gaba da kai hare-haren kan mai uwa da wabi a yankin Zirin Gaza na Palasdinu. Haka na zuwa lokacin da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da gagarumin rinjaye ya bukaci samun tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka Isra'ila tana ci gaba da hare-haren mamaye yankin na Zirin Gaza.