SiyasaJamus
Fafaroma ya bukaci sasanta rikicin Afghanistan
August 15, 2021Talla
Fafaroma na wannan kira ne a daidai lokacin da mayakan Taliban ke shiga Kabul babban birnin Afgahnistan, inda a gefe guda Amirka ke kwashe jami'anta na diflomasiyya a kasar.
Mabiya addinin Kirista dai kalilan ne a Afghanistan, galibi 'yan kasashen waje da ke aikin jakadanci da kuma masu ayyukan jin kai.
Rahotanni daga Afghanistan na cewa ana tattaunawa tsakanin mayakan Taliban da gwamnatin kasar domin ganin yadda za a mika mulki ba tare da zubar da jini ba.
Shekaru 20 da suka gabata ne dai sojojin taron dangi karkashin jagorancin Amirka da kungiyar tsaro ta NATO, suka kifar da mulkin Taliban da ke rike da iko a tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.
Tuni ma Jamus ta snar da rufe ofishin jakadancinta dake birnin Kabul a wannan Lahadi.