1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa ya sake ɓarkewa a Siriya

April 16, 2012

Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun shugaba Bashar al-Assad da masu fafutukar neman sauyi, a daidai lokacin da tawagar sa ido ke fara aikinta a ƙasar.

https://p.dw.com/p/14exg
REFILE - CORRECTING SPELLING COLONEL'S NAME Colonel Ahmed Himmiche (C), a member of a U.N. monitors team, speaks to the media at a hotel in Damascus April 16,2012. A United Nations advance observers' team arrived in the Syrian capital Damascus late Sunday to monitor the fragile cease-fire brokered by international envoy Kofi Annan, causing discussion from all circles in Syria. REUTERS/Khaled al- Hariri (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS)
Hoto: Reuters

Da ma dai ƙasashen yammacin duniya sun nuna shakku game da alƙawarin daina musguna wa 'yan adawa da shugaban na Siriya ya yi.

Tashin bama-bamai da kuma misayar harbe harbe tsakanin sojojin na Siriya da kuma 'yan adawan sun fi ƙamari ne a Homs, sakamakon ɗimbin waɗanda suka bijire ma gwamnati da wannan birnin ya ƙunsa. hasali ma dai, mutane a ƙalla 50 sun rasa rayukansu tun bayan da aka fara aiwatar da shirn wanzar zaman lafiya da tsohon skataren Majalisar Ɗinkin Duniya wato Koffi Annan ya tsara. shugaban bashar al-assada ya zargi masu fafutukar neman sauyi da afka wa sojojinsa dama dai fararen hula da faɗa. Yayin da su kuma 'yan adawan Siriya suka bayyana cewar suna neman kare kawunansu ne daga luguden wuta da sojojin ke yi a biranen Idlib da kuma Homs.

A halin yanzu dai ruƙunin farko na jami'an da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura Siriya domin shiga tsakani sun isa birnin Damascus. Da ma dai wannan tawagar da kanal Ahmed Hammiche na Moroko ke shugabanta ta na daga cikin waɗanda kwamitin sulhu ya amince su bayar da gudun mawa domin a warware rikicin siyayar da ya ki ci ya ki cinyewa a Siriya. Kundirin da mambobin kwamitin sulhu suka albarkanta, ya tanadai tura sojojin hanzar da zaman lafiya guda 250 cikin mako mai kamawa, da kuma jami'an da za su shiga tsakani guda talatin. sai dai a cewar Ahmad Fawzi da ke zama kakakin koffi Annan da ke shiga tsakani, muhumi ba tu anan shi ne rawar da za su iya takawa wajen kawo karshen rikicin.

--- A Syrian forces tank moving along a road during clashes with the Syrian army defectors, in the Rastan area in Homs province, central Syria, on Monday Jan. 30, 2012. Syrian forces heavily shelled the restive city of Homs on Monday, and troops pushed back dissident troops from some suburbs on the outskirts of Damascus in an offensive trying to regain control of the capital's eastern doorstep, activists said. (Foto:AP/dapd) In this Friday, April 6, 2012 photo, Free Syrian Army fighters try to spot a sniper during fighting with Syrian troops in a suburb of Damascus, Syria. Syrian government shelling and offensives against rebel-held towns killed dozens of people across the country on Saturday, activists said, as the U.S. posted online satellite images of troop deployments that cast further doubt on whether the regime intends to comply with an internationally sponsored peace plan. (Foto:AP/dapd)
Hoto: AP

"Mutane da da dama na dasa ayar tambaya game da zahirin abin da mutane shida ko bakwai za su iya yi wajen kwantar da kurara rikicin. Amma dai ina ganin cewar sojojin kiyaye zamn lafiya za su iya shiga tsakani da nufin rage tashe-tashan hankula tsakanin sassa da ke gaba da juna."

Bukatar ɓangarorin biyu su kai zuciya nesa

Amma kuma a nasa ɓangaren, sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki Monn ya yi kira ga gwamnati siriya da kuma 'yan adawa da su kai hankali nesa, tare da guje ma takalat faɗa da kuma faɗace faɗace tsakaninsu. hakazalika ya yi kira ga masu fafutzukar neman sauyi da su bayar da hadin kai ga shirin warware rikicin siyasa na wata da watanni. ko shi ma jakadan syriya a Majalisar Ɗinkin Duniya cewa ya yi matikar ba 'yan adawa ba su tsagaita buɗe wuta ba, to lallai ba za a rabu da bukar ba.

Jafari ya ce" muna zuba ido domin ganin cewar ɗaya ɓangaren ma ya mutunta tsare-tsaren shirin wanzar da zaman lafiya."

Ita dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi fadar mulki ta Damascus ta sakar wa tawagarta 'yancin walwala a cikin kasar domin shaidar da zahirin abin da ke faruwa da nufin daukan matakan da suka weajaba. Tun da farko dai gwamnatin Siriya ta amince tawagar da shiga sako da lugun na kasar, saboda a cewarta ba da da wani abin da za ta boye. Cheikh salman,na cibiyar Brooking da ke bincike kan harkokin siyasar kasashen duniya cewa ya yi dole majalisar dinkin duniya ta yi wannan gargaɗi matukar dai ta na so ta kai labari.

In this image made from amateur video released by the Shaam News Network and accessed Sunday, April 15, 2012, a building is on fire following purported shelling in Homs, Syria. Syrian troops are reported to have shelled residential neighborhoods dominated by rebels in the central city of Homs Sunday, activists said, killing at least three people hours before the first batch of United Nations observers were to arrive in Damascus to shore up a shaky truce. (Foto:Shaam News Network via AP video/AP/dapd) TV OUT, THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Hoto: dapd

"Idan Majalisar Ɗinkin Duniya ta sako sako da wani fannin na shirin, to babu shakka babu ba za ta yi nasara a wannan yunkuri da ta ke yi ba. A nawa tunanin ma dai, sakatare ban ki Moon na kaffa kaffa da rikcin na syiya saboda ya na ganuin cewa akwai lauje cikin nadi."

Dubban yan kasar ta Syriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da manufofin gwamnati a wannan litin da ke zama ranar hutu a syriya. wani faifai video ya nunar da dimbin yabna adawa na daga tuta tare da rera taken goyon baya ga sojojin da suka juya wa shugaba bashar al.Aasdav baya.

Mawallafiya: Mohammed Auwal Balarabe
Edita : Zainab Mohammed Abubakar