Faɗa ta ɓarke a jamho'riyar Afirka ta Tsakiya
July 20, 2010Rahotanin daga jamho'riyar Afirka ta Tsakiya,sun ce wani mumunar faɗa ya rincaɓe a garin Biaro da ke a arewacin ƙasar tsakanin dakarun gwamnati da na ƙungiyar 'yan tawayen CPJP, a daidai lokacin da aka shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dakuma na 'yan majalisu a wannan shekara.
Masu aiko da rahotanin sun ce 'yan tawayen sun kai farmakin ne ga rundunar sojojin ƙasar a yankin,
mako ɗaya da fara yin regista na ƙwance ɗamara dakarun 'yan tawayen a Paoua yankin da ke a arewa maso yammacin ƙasar.
da ya ke magana da kamfanin dilanci labarai na Faransa babban kwamanda dakarun na CPJP Abdullahi Hissene ya shaida cewa sun karɓi iko da garin na Biaro, sanarwa da dakarun gwamnatin suka mussunta.
Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu