1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta yaki hauhawar farashin makamashi

Mouhamadou Awal Balarabe
September 14, 2022

Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi alkawarin samun hadin kan kasashen Turai a yunkurinta na samar da dokar da za ta katse hauhawar farashin wutar lantarki da sauran makamashi.

https://p.dw.com/p/4Gpa2
Frankreich | Ursula von der Leyen im Straßburger Europaparlament
Hoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi tsokaci kan batun hauhawar farashin makamashi bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ke barazana ga tattalin arzikin nahiyar. A jawabinta na sa'a guda a majalisar EU da ke Strasbourg kan halin da kungiyar ciki, ta ce hukumarta za ta kwaskware tsarin kasuwar wutar lantarki, don taimakawa wajen shawo kan hauhawar farashin makamashi.

Yuro biliyan 14 na haraji ne kasashen EU za iya samu daga kazamar riba da kanfofin da ke samar da wutar lantarki ke samu tun bayan fadawa cikin rikici na makamashi, lamarin da Von der Leyen ta ce za a raba ga 'ya'yan na Turai.

von der Leyen ta ce: "A wadannan lokutan ba daidai ba ne a samu kazamar riba ba sakamakon amfana daga yaki da kuma masu amfani da wutar lantarki ba. A cikin wadannan lokutan, dole ne a raba ribar kuma a ba da ita ga wadanda suka fi bukata."