1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta taimaka wa 'yan tawayen Libiya

May 23, 2011

Ƙungiyar EU ta buɗe ofishin jakadancinta a birnin Benghazi cibiyar 'yan tawaye

https://p.dw.com/p/11MGB
Tutar ƙungiyar Tarraya TuraiHoto: AP

►Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta sha alwashin cigaba da tallafawa 'yan tawayen ƙasar Libya da ke fafutukar ganin sun kau da shugaba Ghaddafi daga karagar mulki. Sakatariyar harkokin wajen ƙungiyar Catherine Ashton ce ta baiyana haka lokacin da ta buɗe ofishin jakadancin ƙungiyar a Benghazi da ke gabashin ƙasar ta Libya.

Sakatariyar harkokin wajen ƙungiyar ta Tarayyar Turai ta ce ƙungiyar za ta ba 'yan tawayen na Libya duk irin gudummawar da ta kamata da nufin ganin sun cimma nasarar da su ka sanya a gaba domin kuwa al'ummar ƙasar ta Libya na bayan su a saboda haka ne ma ƙungiyar ta ga dacewar buɗe ofishin jakadancinta a garin Benghazi da ke gabashin ƙasar wanda a halin yanzu 'yan tawayen ƙasar ke iko da shi.Ta kuma nuna jin dadin ta a wani jawabi da ta yi a sa'ilin buɗe ofishin jakadancin na su inda ta ce ta gamsu da irin karsashin da mutanen Libya ke da shi na ganin sun samu sauyin mulki, lamarin da ta ce ya sake zaburar da ƙungiyar wajen dafa mu su da nufin ganin mafarkin su

Ta ce abubuwan da na gani daga filin jirgin saman da na sauka zuwa nan musamman ma dai a jikin fastoci ya nuna irin zage damtsen da jama'ar ƙasar nan su ka yi wajen kawo sauyi, to na zo ne domin in shaida muku cewar ƙungiyar Tarayyar Turai za ta bada cikakakkiyar tallafawa ta tsawon lokaci. Baya ga wannan ta kuma ambata cewar za su taimakawa ƙasar wajen ganin an daidaita al'amura, musamman ma dai sha'anin da ya danganci tattalin ariziƙi.Bayan buɗe ofishin jakadancin da ta yi, ta kuma kewaya cikin garin na Benghazi da nufin gane wa idon ta yadda lamura ke tafiya.Kazalika ta yi wata tattaunawa ta musamman da Mustafa Abul Jalil wanda ke zaman shugaban 'yan tawayen na Libya. Jim kaɗan bayan kammala tattaunawar ta su, Mr. Abduljalil ya nuna gamsuwar sa dangane da wannan matsayi da ƙungiyar ta ɗauka gami da yi wa mata godiya.Masu sharhi kan al'amuran ƙasar ta Libya dai na ganin wannan ziyarar ta da Catherine Ashton ta yi gami da buɗe ofishin jakadancin ƙungiyar ta tarayyar turai a matsayin wani ƙarin ƙarfin gwiwa ga 'yan tawayen, wanda su ka jima su na zawarci tare kuma da da neman amince wa da su a mastayi gwamnatin riƙon ƙwarya.

Da ta ke maida martani game da buɗe ofishin da kuma goyon bayan da ƙungiyar ta EU ta ba 'yan tawayen, gwamnatin shugaba Ghaddafi ta baiyana shi a matsayin amince wa da wata haramtaciyyar ƙungiya, inda ƙara da cewar hakan na iya sawa a sake samun ƙarin tsamin dangantaka tsakanin wasu kasashen na turai da ƙasar ta Libya.To gabanin bikin na buɗe ofishin jakadancin EU a ƙasar ta Libya dai, jiragen yaƙin dakarun ƙawance na NATO sun kai famaki tashar jiragen ruwa da ke Tripoli da kuma gidan Shugaba Ghaddafi.

Wani ɗan jarida da ya ganewa idon sa farmakin da aka kai ya ce ya ji ƙarar fashewar bamabamai har sau biyu kuma ya ga wani jirgin yaƙi na shawagi ƙasa-ƙasa a Tripoli, lamarin da ya tabbatar da cewar dakarun NATO na ci-gaba da yin luguden wuta kan dakarun da ke biyayya ga Shugaba Ghaddafi.Baya ga wanna kuma, dakarun na NATO sun kai farmaki kan wani sansanin sojin ruwa da ke Sirth wadda ke zaman mahaifar Ghaddafi kazalika nan gaba ana sa ran kai wasu hare-haren musamman ma dai ga abin da ya danganci dakarun na Ghaddafi.

A ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi : Salisu Ahmed
Edita : Abdourahamane Hassane