1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Turai za su tabka mahawara a kai

Zainab Mohammed Abubakar
June 21, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanar da fara tattaunawa da hukumomin MDD, dangane da kafa cibiyoyin tantance 'yan gudun hijira a kasashen da ke yankin Arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/301NV
Italien Symbolbild Rettung von Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/A. Paduano

Sai dai ta jaddada cewar, ba ta da niyar samar da wuri makamancin sansanin gwale gwale na Guantanamo ga 'yan gudun hijirar. Hukumar gudanarwa ta EU ta ce cikin tsarin, an sanya dukkan matakai na kariya ga 'yan gudun hijirar da aka ceto daga cikin Teku a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

A mako mai zuwa nedai ake saran mahawara kan wannan batu a taron Kungiyar Tarayyar Turai da zai gudana a birnin Brussels din kasar Beljium.

Amurka ta fuskanci fushin kasashen duniya lokacin da ta fara amfani da sansanin sojin ruwanta da ke Guantanamo a kasar Kuba, wajen azabtar da wadanda take zargi da ta'addanci, tun bayan hare haren 11 ga watan Satumban 2011 a kasar.